Home Labarai Ba mu da bukatar rundunar Shege ka Fasa a Kano – Ganduje

Ba mu da bukatar rundunar Shege ka Fasa a Kano – Ganduje

71
0

Gwamnatin jihar Kano ta nisanta kanta da kirkiro rundunar tsaron jihohin Arewacin Nijeriya da ake yiwa taken ‘Shege Ka Fasa’.

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da ‘yan jaridar fadar shugaban kasa a yau Juma’a, jim kadan bayan ganawar sa da shugaba Buhari karkashin rakiyar wasu manyan jihar.

Ganduje ya ce gwamnatin jihar sa ta yi shiri mai karfi kan harkar tsaro a don haka bata bukatar wani sabon tsari kuwa, domin tsarin da take kai, ya sanya jihar ta zama tamkar lahirar masu aikata laifi.

Ya kara da cewa jihar ta samar da kyakkyawan yanayi ga hukumomin tsaro, yana mai cewa jihar ta samar da cibiyar tsaro, wadda hukumomin tsaron ke saduwa da juna.

Baya ga haka, ya ce jihar ta kashe kimanin Naira miliyan 500 cibiyar horas da sojoji a dajin Falgore, wanda ya kasance mafi girma a Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply