Home Sabon Labari Ba mu da wata kungiyar yan sintiri, inji fulani mazauna Kudancin Nijeriya

Ba mu da wata kungiyar yan sintiri, inji fulani mazauna Kudancin Nijeriya

73
0

Daga Abdullahi Garba Jani

Kungiyar Fulani ta Miyetti Allah a jihar Ondo, ta ce babu kanshin gaskiya a cikin labarin da ake yadawa cewa ta kafa wata kungiyar sintiri ta Vigilante a jihar.

Shugaban kungiyar na jiha Alh Gabar Garba ya fada wa manema labarai cewa kungiyarsu ba za ta taba yi wa dokar kasa karan-tsaye ba.

Kungiyoyi  da masu ruwa da tsaki na ta kokarin ganin bangaren Fulani makiyaya da ‘yan sintirin Vigilante da kuma manoma sun zauna lafiya ba tare da hantara ko kyarar juna ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply