Home Labarai Ba mu san ina Kyari yake ba – Gwamnatin Lagos

Ba mu san ina Kyari yake ba – Gwamnatin Lagos

81
0

Kwamishinan lafiya na jihar Lagos Farfesa Akin Abayomi, ya ce bai san inda shugaban ma’aikata na fadar shugaban kasa Abba Kyari ya shiga ba, sabanin rahotannin da ake yadawa na cewa yana asibitin da ake kebance wadanda suka kamu da cututa ta Mainland da ke Lagos.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi dai, Kyari ya ce an tabbatar yana dauke da cutar kuma zai koma Lagos a ranar Litinin domin karin wasu gwaje-gwaje da shawarwari.

Kwamishinan lafiyar ya ce a ko wace rana ana yin gwajin cutar coronavirus 150 a asibin Yaba da ke Lagos.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply