Home Lafiya Ba mu so a riƙa gwajin cutar HIV kafin aure- inji wata...

Ba mu so a riƙa gwajin cutar HIV kafin aure- inji wata ƙungiya

157
0

Abdullahi Garba Jani/Banye

 

Gamayyar ƙungiyoyin wayar da kan jama’a game da cuta mai karya garkuwar jiki HIV/Aids watau ‘ Coalition of Civil Society Network for HIV/AIDS in Nigeria’ a turance ta yi kira ga malaman addini da su dakatar da wajabta gwajin cutar HIV kafin aure a tsakanin ma’aurata.

Hotan alamar cutar HIV

Ƙungiyar ta ce, ci gaba da hakan zai haddasa tsangwama da kuma karya dokar hana tsangwama ga masu ɗauke da cutar.

Shugaban ƙungiyar Ikenna Nwakamma ya yi wannan kiran a Abuja, lokacin da ya ke ganawa da kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya -NAN .

Ya yi nuni da cewa ya kamata a daƙile dukkanin hanyoyin da za su kawo tsangwama da ƙyamar da ake nuna wa masu ɗauke da cutar ta HIV/AIDS.

Yadda ake gwajin cutar HIV

Mr. Ikenna ya ce wannan gwajin da malaman addini ke tursasawa na ƙara rura wutar ƙyama, wanda hakan ya ci karo da dokar hana tsangwama ta 2014.

Ya ce a kwana-kwanan nan suka samu labarin wani malamin lafiya ya ba da rahoton ƙarya game da cutar HIV kan wani da ya je gwajin.

Mr Ikenna ya ci gaba da cewa idan har malamin lafiya zai iya wannan aika-aikar, to kuwa babu dalilin da zai sa a kawo tsarin cikin al’umma da zai haddasa ma ta ruɗani.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply