Home Labarai Ba mu yarda da rushe ƙananan hukumomi – APC Zamfara

Ba mu yarda da rushe ƙananan hukumomi – APC Zamfara

54
0

Jam’iyyar APC a jihar Zamfara ta yi watsi da matakin majalisar dokokin jihar na rushe shugabannin ƙananan hukumomi.

A makon da ya gabata ne dai majalisar ta rushe zaɓabɓun shugabannin ƙananan hukumomin jihar su 14, saboda zargin su da almubazzaranci da kuma kasa yaƙar ƴan bindiga.

Saidai a wata sanarwa da shugaban jam’iyyar APC na jihar Alhaji Lawal Liman ya fitar, ya ce matakin majalisar ya saɓawa kundin tsarin mulkin Nijeriya.

Liman ya ce jam’iyyar za ta bi matakin shari’a don bin kadin al’amarin.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply