Shugaban kwamitin da aka kafa don binciken dakataccen mukaddashin shugaban hukumar EFCC Mai Shari’a Ayo Salami ya ce ba rana ba lokacin kammala binciken Ibrahim Magu.
Ayo Salami wanda tsohon shugaban kotun daukaka kara ta Nijeriya ne, ya yi wannan furucin ne a lokacin da ya ke ganawa da jaridar Punch.
A lokacin da jaridar ta tambaye shi, ko yaushe za a kammala binciken Ibrahim Magu, sai ya ce ba ya da masaniya akai.
