Home Labarai Ba ruwanmu da batun komawa makaranta, yajin aiki muke yi – ASUU

Ba ruwanmu da batun komawa makaranta, yajin aiki muke yi – ASUU

202
0

Akwai yiwuwar batun komawa makarantu ya samu tsaiko ganin yadda kungiyar malaman jami’o’i ta Nijeriya ASUU take neman yin turjiya da batun bisa dalilin cewa gwamnatin tarayya ta gaza cika musu alkawurransu.

Shugaban kungiyar ta ASUU Prof Biodun Ogunyemi, ya shaida wa jaridar Vanguard cewa yajin aikin kungiyar zai ci gaba har sai gwamnati ta mutunta yarjejeniyarsu.

Prof Biodun ya ce duk da dai gwamnati ta gayyace su wata ganawa, to amma ba su san abin da za a tattauna ba, bare a cimma matsaya.

Ya kara da cewa muddin ba su cimma wani tartibin bayani ba kafin ranar bude makarantun, to kuwa za su ci gaba da yajin aikinsu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply