Home Sabon Labari Ba ‘yan Nijeriya a jerin ‘yan wasa 10 masu tsada a Afirika

Ba ‘yan Nijeriya a jerin ‘yan wasa 10 masu tsada a Afirika

120
0
LIVERPOOL, ENGLAND - JANUARY 02: Mohamed Salah of Liverpool celebrates with Sadio Mane after scoring his team's first goal during the Premier League match between Liverpool FC and Sheffield United at Anfield on January 02, 2020 in Liverpool, United Kingdom. (Photo by Clive Brunskill/Getty Images)

Rahotanni sun nuna cewa babu sunan dan wasann Super Eagles ta Nijeriya ko daya, a jerin sunayen ‘yan wasan Afika 10, mafiya tsada.

Jerin sunayen wadanda transfermatkt.com ta wallafa, ya nuna kasashen Senegal, Ivory Coast da Morocco na da ‘yan wasa biyu ko wanen su.

Daga cikin sunayen kuma, akwai ‘yan wasan kasashen Masar, Gabon, Algeria da Ghana.

‘Yan wasan Liverpool Mohammed Salah da Sadio Mane sune kan gaba inda ko wanen su ke da darajar Euro Miliyan 120, a sai dan wasan Arsenal Pierre-Emerick Aubameyang da na Napoli Kalidou Koulibaly da suka zo na uku, suna da darajar Euro Miliyan 56 ko wanen su.

Achraf Hakimi wanda a kwanan nan ya koma Inter Milan daga Real Madrid ya zo na biyar kan darajar Euro Miliyan 54.

Dan wasan Arsenal Nicolas Pepe, Riyad Mahrez na Manchester City da Wilfred Zaha na Crystal Palace, sune suka zo na shida, da na bakwai da takwas, kan Euro miliyan 52, 48, da kuma 44.

Dan wasan Atletico Madrid Thomas Partey shi ne na 9, tare da Hakim Ziyech da bai jima da dawo Chelsea ba, inda suke da darajar Euro miliyan 40.

Dan wasan Nijeriya da ya tabuka wani abu shi ne Wilfred Ndidi na Leicester City wanda ya zo na 12, da darajar Euro miliyan 36.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply