Tsohon gwamnan jihar Sokoto Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, ya ce matuƙar ana son ganin bayan ƴan bindiga a sai an tsananta hare-haren soji.1q
Sanatan wanda shi ne shugaban kwamitin tsaro na majalisar dattawan Nijeriya, ya ce kai hare-hare ba ƙakƙautawa kan ƴan bindigar da suka addabi yankin Arewa maso yammacin Nijeriya, zai taimaka wajen daƙile tasirin su.
Da yake zantawa da Jaridar Daily Trust, Wamakko ya kuma yi kira ga gwamnonin jihohin da abun ya shafa, da su daina sulda ƴan bindigar domin hakan na ƙara masu ƙwarin gwiwa.

Ai gaskiya a nawa ra, ayin kam sulhu da yan bindiga bazai kawo karshen ayyuykan su ba.
babbar matsalar shugaban kasa yar aduwa shine ya fara sulhu da yan ta’addan Niger delta kuma akayi musu duk abunda sukeso
to miya su kuma yan arewa baza’a musu hakan ba
hatta boko haram ansha Sulhu dasu
amman antaba magana?
Wannan maganar haka take Allah ya kawo muna karshen su