Home Labarai Ba za mu ɗauki matakin rufe jihohi ba – Gwamnonin Arewa

Ba za mu ɗauki matakin rufe jihohi ba – Gwamnonin Arewa

145
0

A jiya Litinin ne, Kungiyar Gwamnonin Arewa suka gudanar da wani taro domin tattaunawa kan illar da annobar Cutar Coronavirus za ta iya yiwa yankin.

Taron dai an gudanar da shi ne ta hanyar Tangaraho, inda shugaban kungiyar gwamnonin a Arewacin Nijeriya kuma gwamnan jihar Plateau Simon Lalong ya jagoranta, ya basu damar tattaunawa kan abubuwan dake faruwa a yanzu, da kuma matakan da suke dauka don dakile yaduwar cutar.

A cikin wata sanarwa da Daraktan yada Labaran gwamnan Lalong Dr Macham Makut ya fitar ya bayyana cewa, bayan rahotannin da Kungiyar ta tattara, gwamnonin sun yanke shawarar tsaurara matakan da suka dauka na dakile yaduwar cutar ta hanyar rufe iyakokin jahohin da hada kai tsakanin su don ganin sun cimma wannan burin.

Sanarwar ta kara da cewa, kowace jaha zata dauki matakan da suka dace da yanayin ta, inda suka ce rufe jahohin shine mataki na karshe da za su iya dauka, kasancewar da yawa daga cikin mutanen yankin manoma ne, wanda dole su fita gona kuma ga shi ruwan sama ya fara sauka.

Sauran batutuwan da suka tattauna sun hada da na bada tallafi domin rage radadi, inda suka bayyana rashin jin dadin su kan yadda har yanzu babu wata jiha a yankin da ta samu wani tallafi, duk kuwa da cewa an samu bullar cutar a wasu daga cikin su, inda sauran ke iya bakin koarin su don ganin cutar bata bulla a jahohin su ba.

Abu na gaba da suka bayyana damuwar su akai shine rashin cibiyoyin gwajin cutar ko daya a yankin, inda suka yi matsayar cewa za su hada kai da gwamnatin tarayya wajen ganin kowace jiha ta samu koda cibiya 1 ce, inda masu yawan jama’a kuma za su samu 2.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply