Home Labarai Ba za mu hana amfani da intanet ba – Gwamnatin tarayya

Ba za mu hana amfani da intanet ba – Gwamnatin tarayya

140
0

Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed ya bayyana cewa sabanin yadda wasu mutane ke yadawa, gwamnatin tarayya ba ta da nufin hana al’umma yin amfani da kafafen intanet.

Ya bayyana cewa gwamnati na sane da irin rawar da kafafen ke takawa wajen kawo ci gaba cikin al’umma, sai dai hakan ba zai sa gwamnatin ta zuba ido ana amfani da ita ba kara zube.

Ministan da yake jawabi a jiya cikin birnin Ikko, ya shaida cewa ta intanet ne labaran karya ke tafiya kamar gobarar daji, wanda ya bayyana a matsayin abinda ke kara tunzara harkar tsaro a kasar nan.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply