Home Labarai Ba za mu lamunci duk wani nau’in cin zarafin mata ba –...

Ba za mu lamunci duk wani nau’in cin zarafin mata ba – NAWOJ Katsina

359
0

Kungiyar mata ‘yanjarida ta kasa reshen jihar Katsina NAWOJ ta ce akwai bukatar hada hannu wuri guda domin yakar duk wani yunkuri na cin zarafin mata a kasar nan.

A jawabinta na bikin yakar cin zarafin mata na bana, 2020, Haj Hannatu Muhammad, shugabar kungiyar ta NAWOJ a Katsina, ta yi kira ga mahukunta, da su dabbaka dukkanin dokokin da suka yi hani da cin zalin din mata a kasar nan.

Hannatu Muhammad ta ce ya kyautu gwamnati ta saka idanu don ganin an hana aikata fyade, safarar mata, auren dole da mugunyar dabi’ar nan ta yi wa mata kaciya a cikin al’umma.

Shugabar kungiyar ta NAWOJ ta jihar Katsina ta yi kira ga mata da su rika bayyana irin cin zarafin da aka yi musu domin daukar matakin da ya da ya dace akan kari.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply