Home Labarai Ba za mu zura ido muna gani ana mana cin kashi ba...

Ba za mu zura ido muna gani ana mana cin kashi ba – Buhari

157
0

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ba zai amince ba ƴan daba su ƙwace ragamar tafiyar da harkokin ƙasar nan ba.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a yayin taron da ya yi ta na’urar bidiyo da tsaffin Shugabannin ƙasar a Abuja.

Ya kuma jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta zura ido ba tana kallon ɓata gari suna yin abinda suka ga dama ba.

Ya ce gwamnati ta ji ƙorafe-ƙorafen masu zanga-zangar, inda har ta gaggauta ɗaukar mataki na soke rundunar ƴan sanda ta SARS kamar yadda su ka buƙata.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply