DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, October 9, 2026
HomeBabban Labari Ba zan bai wa Tinubu kunya ba, zan tabbatar APC ta yi...

Ba zan bai wa Tinubu kunya ba, zan tabbatar APC ta yi nasara a 2027 – Abdulaziz Yari

Sanata Abdulaziz Yari Abubakar ya amince da naɗin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi masa na zama Darakta-Janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC na zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Yari, wanda ke wakiltar Zamfara ta Yamma a majalisar dattawa, ya bayyana godiyarsa ga Shugaba Tinubu da shugabannin APC bisa amincewa da shi da wannan babban nauyi.

Fadar Shugaban Nijeriya ta bayyana cewa Shugaba Tinubu ne zai jagoranci kwamitin a matsayin Shugaba, yayin da mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima, zai kasance mataimakin shugaban kwamitin na farko.

A cikin tsarin kwamitin, an naɗa Gwamnan jihar Imo, Sanata Hope Uzodimma, a matsayin Sakataren kwamitin, yayin da Yari zai jagoranci ayyukan yaƙin neman zaɓen a matsayin Darakta-Janar.

A cikin wata sanarwa, Yari ya ce ya karɓi nauyin kuma yana matuƙar godiya da kuma sanin girman alhakin da aka ɗora masa.

Ya ce: “Ina matuƙar godiya ga Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar bisa amincewar da suka yi da ni, ba zan ɗauki wannan amana da wasa ba.”

Tsohon gwamnan jihar Zamfara ya bayyana cewa yaƙin neman zaɓen 2027 ba zai kasance kawai fafatawar neman kuri’u ba, sai dai wata dama ce ta tattaunawa da al’ummar Nijeriya kan makomar ƙasar.

Yari ya yi alƙawarin gudanar da yaƙin neman zaɓen cikin haɗin kai, ladabi da mutunta dukkan ’yan Nijeriya, yana mai cewa za a fara aikin nan take.

Ya kuma yi kira ga ’yan Nijeriya ba tare da la’akari da jam’iyyarsu ba, da su zaɓi ci gaba maimakon rarrabuwar kai, yana mai cewa APC za ta nemi amincewar jama’a ne bisa abubuwan da ta cimma, ba hayaniya ba.

Yari ya kammala da cewa da yardar Allah da ƙoƙarin shugabannin jam’iyya da magoya bayanta, APC za ta samu nasara a zaɓen shugaban ƙasa na watan Janairun 2027.

RELATED ARTICLES

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata