Home Labarai Ba zan hana zanga-zangar lumana ba – Buhari

Ba zan hana zanga-zangar lumana ba – Buhari

149
0

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, ya ce gwamnatinsa ba za ta hana matasa ‘yancinsu na yin zanga-zangar lumana ba, sai dai ya gargade su da su yi hattara da wadanda za su iya yin amfani da damar don cimma wata manufarsu ta daban.

Jaridar “Muryar ‘Yanci” ta rawaito cewa, Buhari ya faɗi haka ne, lokacin da ya ke ganawa da Ministan Matasa da wasanni Sunday Dare, a Abuja.

Sunday Dare, wanda ya gana da’yanjaridar fadar shugaban ƙasa jim kadan bayan kammala ganawar, ya ambato Buhari na shawartar matasan, da su yi hattara da bata gari wadanda za su yi amfani da damar wajen bata kyakkyawar niyyar matasan.

Ministan wanda ya ce ya zo ne don sanar da shugaban ƙasar halin da ake ciki kan masu zanga-zangar EndSARS, ya ce shugaban kasar ya ba matasan tabbacin cewa za a aiwatar da bukatunsu biyar da suka gabatar wa gwamnatin tarayya ta hannun wakilan su.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply