Home Labarai Ba zan kara tsayawa takara ba, inji Sanata Danjuma Goje

Ba zan kara tsayawa takara ba, inji Sanata Danjuma Goje

92
0

Abdullahi Garba Jani

Tsohon gwamnan jihar Gombe kuma Sanata mai wakiltar Gombe ta tsakiya a majalisar dattawa ta Nijeriya Danjuma Goje ya ce ba zai sake neman wani mukamin siyasa na tsayawa takara ba.

To sai dai ba ta nuna ba, amma ta yi shudi, Sanata Goje ya ce zai ci gaba da kasancewa a cikin sha’anin siyasa.

Tsohon gwamnan na magana ne a wajen taron ba da tallafi a garin Pantami, inda ya ce ya gode Allah da Ya ba shi ikon rike mukamin Sanata bayan da ya kwashe shekaru 8 a bisa kujerar gwamna, da mukamin kwamishina da kuma na minista.

Ya ce zai ci gaba da tsoma hannu a dukkanin harkokin siyasa, amma dai ba zai sake neman tsayawa takara ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply