Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya ce ba zai yadda ya fara kawo maganar sake tsayawa takara a karo na uku ba. Ya ce bayan shekarunsa sun ja, shi musulmi ne kuma ya rantse da Al-Qur’ani mai girma akan zai martaba kundin tsarin mulkin Nijeriya.
Shugaban ya fadi haka ne a wurin taron majalisar zartaswa na jam’iyyar APC da ya gudana a Abuja. Shugaban kasar ya fada musu cewa ya san yana zangonsa na karshe a don haka ba zai yi gangancin neman zango na uku ba.

Sai dai a wurin taron shugaba Buhari ya ce zai so jam’iyyarsa ta APC ta ci gaba da mulkin Nijeriya har bayan saukarsa daga kujerar shugabanci. Ya ce idan har ‘ya’yan jam’iyyar suka yi sakaci gwamnati ta subuce musu a karshen zangonsa na biyu to tarihi ba zai mance irin wannan sakaci ba.
