DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, October 14, 2026
HomeSiyasaBabban aikina shi ne sanya wa jagororin adawa hawan jini — Wike

Babban aikina shi ne sanya wa jagororin adawa hawan jini — Wike

Ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ce babban aikinsa a siyasa da ake yi gabanin zaɓen 2027 shi ne sanya jagororin jam’iyyun adawa cikin matsin lamba, ta yadda ba za su samu sukuni ba.

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa Wike ya bayyana hakan ne ranar Juma’a yayin da yake zantawa da manema labarai a lokacin duba wasu ayyukan da ake gudanarwa a Abuja.

Wike ya ce rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar PDP ya sa ya zama da wahala a bayyana wata jam’iyyar adawa guda ɗaya da za a iya ɗauka a matsayin jagorar hamayya mai ƙarfi a zaɓen 2027.

Ya ce a halin da ake ciki, ba a iya ganin wata jam’iyyar adawa mai ƙarfi da za ta iya zama babbar barazana ga jam’iyyar APC mai mulki.

Ministan ya bayyana cewa ba ya damuwa da yadda shugabannin adawa ke ji game da irin rawar da yake takawa a siyasar ƙasar, yana mai cewa ba aikinsa ba ne ya tabbatar sun ji daɗi.

Wike ya ce: “babban aikina shi ne tabbatar da cewa ba su ji daɗi ba a kowace rana, domin hakan zai sanya su cikin matsin lamba.”

Ya ƙara da cewa idan mutum yana fafatawa da wani a siyasa, ba aikinsa ba ne ya sauƙaƙa wa abokin hamayyarsa, illa dai ya yi ƙoƙarin kayar da shi sosai.

Ministan, wanda tsohon gwamnan jihar Rivers ne kuma ɗan jam’iyyar PDP, ya daɗe yana cikin sabani da wasu manyan ƴan siyasar adawa sakamakon rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam’iyyar.

Da yake magana kan tsohon mataimakin shugaban Nijeriya, Atiku Abubakar, da ɗan takarar shugaban ƙasa na Labour Party a 2023, Peter Obi, Wike ya ce ba ya damuwa da yadda suke kallon sauye-sauyen siyasar da ake samu.

Ya ce idan ya san yadda suke ji a yanzu, hakan ma zai iya ƙara masa ƙarfin guiwar matsa musu lamba da ƙara rikicin siyasar da ke tsakaninsu.

Wike ya ce manufarsa ita ce ganin cewa abokan hamayyarsa ba su samu sauƙin tafiyar da siyasar 2027 ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata