Home Labarai Babbar mota ta latse miji da mata

Babbar mota ta latse miji da mata

110
0

Wani hatsarin mota ya yi sanadiyyar mutuwar wasu mutane biyu da ake kyautata zaton mata da miji ne akan hanyar Sagamu-Ogijo.

Hatsarin dai ya afku ne tsakanin mota kirar Toyota Camry da wata katuwar mota da kuma mai babur.

Mai magana da yawun jami’an tabbatar da bin doka da ka’idojin tuki na jihar Ogun Babatunde Akinbiyi ne ya tabbatar da lamarin ga Kamfanin Dillancin Labarai Na Nijeriya a birnin Abeokuta.

Akinbiyi yace yace hatsarin ya afku ne ta dalilin mugun gudu da tukin ganganci da mai babur din ya yi, wanda ko lamba bai da ita, kuma birkinsa ya shanye.

Yace babur din ya tunkuyi motar kirar Toyota Camry, sai kuma babbar motar dakon kayan ta tattake mutane biyun da ke bisa babur din bayan sun fado kasa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply