Home Labarai Babbar Sallah: APC da PDP a Nijeriya sun fitar da sanarwa mai...

Babbar Sallah: APC da PDP a Nijeriya sun fitar da sanarwa mai ma’ana daya

59
0

Hannatu Mani Abu/AGJ

Jam’iyyar APC mai mulki da ta adawa ta PDP a Nijeriya sunyi kira ga masu hannu da shuni a kasar da su taimaka wa mabukata a wannan lokaci na gudanar da bukukuwan babbar sallah.

Jam’iyyar APC a wata takarda da sakataren watsa labaran jam’iyyar na kasa ya sanya wa hannu Issa Onilu, ya shawarci ‘yan Nijeriya da su yi koyi da koyarwar addinin Islama na sadaukar wa da cika alkawari kamar yadda annabi Ibrahim ya yi.

Lanre yace ‘yan Nijeriya su guje wa duk wani abu da zai nemi dagula zaman lafiyar kasar nan kamar yadda wasu marasa kishin kasa ke neman yi a kwanan bayan nan.

Sannan ya kara da cewa al’ummar musulmi da ‘yan Nijeriya, ya yin gudanar da bikin Sallah babba tare da yan’uwa da abokan arziki su nuna halin kauna ga daukacin al’umma tare da taimaka wa marasa karfi.

Haka zalika, jam’iyyar adawa ta PDP ta bukaci ‘yan Nijeriya da su yi amfani da wannan lokaci na bikin sallah wajen mika al’amuran su ga Allah a kowane lokaci.

Sanarwar ta fito daga bakin mai magana da yawun jam’iyyar ta PDP Kola Ologbondiyan.

Kola yayi kira ga ‘yan Nijeriya da su yi amfani da wannan dama ta sallah babba wajen yin addu’a ga samun yawaitar zaman lafiya a kasar tare da taimakawa mabukata musamman a yankunan da ke akwai yan gudun hijira.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply