Daga Abdullahi Garba Jani
Shugaban Nijeriya Muhammad Buhari ya isa mahaifarsa garin Daura da yammacin Juma’a don gudanar da babbar sallah.
Shugaba Buhari ya isa filin jirgin sama na Umaru Musa ‘Yar’adua da ke Katsina tare da mukarrabansa inda daga bisani ya wuce zuwa birnin Daura ta jirgi mai saukar-ungulu.
A ranar Lahadi dai ne musulmin Nijeriya za su bi sahun ‘yan’uwansu na duniya wajen gudanar da babbar sallah ta wannan shekara.
Rundunar ‘yansandan jihar Katsina cikin wata takarda a Katsina, ta kara nanata kudirinta na tsaurara tsaro a fadin jihar.
