Home Labarai Babbar sallah: Ganduje ya yafe wa ‘yan gidan yari 29

Babbar sallah: Ganduje ya yafe wa ‘yan gidan yari 29

157
0

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yafe wa ‘yan gidan yari 29 da ke tsare a gidan yarin Gwauron Dutse, Kano.

Gwamnan wanda ya ba da umurnin da a saki mutanen a lokacin da ya kai ziyara a gidan yarin, yace matakin na daga cikin bukukuwan babbar sallah.

Ganduje yace an zabo wadanda aka yafe mawar ne ta la’akari da girman laifukan da suka aikata da kuma yadda suke mu’amala a gidan yarin.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply