Home Labarai Babbar Sallah: Gwamnati ta bayar da hutun sallah

Babbar Sallah: Gwamnati ta bayar da hutun sallah

72
0

Daga Abdullahi Garba Jani

Gwamnatin tarayya a Nijeriya ta ware ranakun Litinin da Talata 12 da 13 ga wannan watan na Agusta a matsayin ranakun hutun babbar sallah a kasar.

Babbar sakatariya a ma’aikatar kula da harkokin cikin gida Mr Georgina Ehuriah ta hannun mai magana da yawun ma’aikatar Muhammad Manga, ce ta shaida wa kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya haka a Abuja.

A cikin takardar, ta yi kira ga ‘yan Nijeriya da su amfani da wadannan lokuttan don adu’o’in dorewar zaman lafiya da kaunar juna a kasar.

Sannan ta yi kira ga ‘yan Nijeriya da su guji aikata duk wani abu da kan iya kawo tashin hankali a cikin kasar don tabbatar an samu ci gaban da ake bukata.

Sakatariyar Gwamnatin Tarayya Abuja

Mr Ehuriah ta ci gaba cewa an umurci jami’an tsaron da ke karkashin ma’aikatar da su tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a yayin da kuma bayan bukukuwan sallar.

Kazalika, takardar ta taya al’umma musulmi murnar zagayowar babbar sallah a kasar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply