Home Labarai Babbar Sallah: Sarkin Musulmi ya bukaci da duba jinjirin watan Dhul-hijja yau.

Babbar Sallah: Sarkin Musulmi ya bukaci da duba jinjirin watan Dhul-hijja yau.

84
0

Daga Abdullahi Garba Jani

Mai alfarma Sarkin Musulmi  kuma Shugaban Majalisar Koli ta harkokin Addinin Musulumci Alhaji Sa’ad Abubakar  (iii) ya umurci al’umma musulmi a Nijeriya da su fara duba jinjirin watan Dhul-hijja 1440 A.H  a yau Alhamis.

 

A wata takarda daga shugaban kwamitin kula da harkokin addinin musulunci na fadar sarkin musulmi Farfesa Sambo Wali Junaid, Sarkin Musulmi ya shawarci al’umma musulmi da su kai rahoton ganin jinjirin watan ga masarautar da ke kusa da su, don aikewa ga fadarsa da ke Sokoto.

 

 

Takardar ta kara da shawartar Musulmi da su ci gaba da adu’o’in dorewar zaman lafiya a Nijeriya bakidaya.

 

Watan Dhul-hijja dai shi ne wata na 12 a kalandar musulunci, da ake gudanar aikin hajji don sauke farali da kuma gudanar da babbar sallah (Eid-el-Kabeer). Ana kuma yin babbar sallah a rana ta goma a cikin watan na Dhul hijja

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply