Home Sabon Labari Ba adalci a gina jami’ar sufuri a mahaifar Shugaba Buhari – Bugaje

Ba adalci a gina jami’ar sufuri a mahaifar Shugaba Buhari – Bugaje

27794
0

Dr Usman Bugaje dan gwagwarmayar siyasa a jihar Katsina kuma tsohon na hannun damar Shugaba Buhari ya bayyana cewa ginin jami’ar sufuri da ake yi a garin Daura, mahaifar Shugaba  Buhari sam bai kamata ba.

Bugaje ya bayyana haka ne a yayin wata hira da aka yi da shi a Sashen Hausa na gidan rediyon Muryar Amurka, VOA.

“Ba a dade da cewa za a gina makarantar koyan kimiyya da fasaha a garin na Daura ba, kuma ace za a kara kai masu jami’ar sufuri, gaskia yin hakan babu adalci a ciki” in ji Dr Usman Bugaje.

Tuni al’ummar yankin na Daura suka fara mayar da martani da ma yin shagube ga Dr Bugaje a shafukansu na sada zumunta.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply