Kamar yadda ƙudirin kasafin kuɗin shekarar 2021 ya nuna, hukumar zaɓen Nijeriya INEC, za ta kashe Naira Biliyan ₦40bn a cikin shekarar.
A ranar 8 ga watan Oktoba ne dai shugaba Buhari, ya gabatar da ƙudirin kasafin kuɗin a gaban majalisar dokokin ƙasar, wanda ya kai ₦13.08trn.
Saidai kuma, babu bayanan yadda INEC, za ta kashe waɗannan kuɗi ₦40bn, a cikin gundarin bayanin yadda ƙudirin kasafin kuɗin yake.
A maimakon haka, a cikin layi guda ne kacal aka yi bayanin kasafin na INEC, kamar yadda aka yi ga kasafin majalisar dokokin ƙasar wanda shima ya kai ₦128bn.
