Home Labarai Babu jihar da ta kai mu yaƙi da cin hanci – Ganduje

Babu jihar da ta kai mu yaƙi da cin hanci – Ganduje

166
0

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya ce babu jihar da ta kai su yaƙi da cin hanci a Nijeriya, kasancewar jihar ce kaɗai ke da hukumar yaƙi da cin hanci mai ƙarfi.

Gwamnan ya bayyana haka ne wajen bikin ranar hukumomin yaƙi da cin hanci ta duniya, da aka gudanar a cibiyar yaƙi da cin hanci da ke Kano.

Ganduje, wanda Kwamishinan shari’a na jihar Barrister Lawan Musa Abdullahi ya wakilta, ya ce samar da hukumar sauraron ƙorafe-ƙorafen jama’a da yaƙi da cin hanci da kuma cibiyar yaƙi da cin hanci ya tabbatar da yadda gwamnatin ke goyon bayan ƙoƙarin gwamnatin tarayya na yaƙi da matsalar.

Sauran wakilan hukumomin yaƙi da cin hanci na EFCC ICPC da NHRC sun yaba da ƙoƙarin hukumar yaƙi da cin hanci ta jihar, da suka ce ta jajirce kan aiki tsawon shekaru.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply