Home Labarai Babu Nijeriya a jerin ƙasashe 25 da bankin IMF ya yiwa lamuni

Babu Nijeriya a jerin ƙasashe 25 da bankin IMF ya yiwa lamuni

135
0

Hukumar gudanarwar Bankin bada Lamuni na Duniya IMF, ya amince da gaggauta sassautawa kasashe 25 da suke mu’amala a tsakanin su bashin da yake bin su, a karkashin shirin sa na bada tallafin rage radadi ga kasashen.

Manajan Daraktar Bankin Mrs. Kristalina Georgieva ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar a Birnin Washigton DC na kasar Amurka.

A cewar ta, sun yi wannan sassaucin ne ne domin baiwa kasashen damar yakar annobar cutar Covid-19 da ake fama da ita.

Ta bayyana cewa, an yi masu wannan sassaucin ne domin a taimakawa Talakawa da masu karamin karfi dake kasashen, inda aka daga masu kafa har nan da watanni 6 masu zuwa.

Ta ce hakan zai taimaka masu wajen magance matsalar kudin da suke da shi, musamman ma wajen yaki da cutar Coronavirus.

Kasashen da zasu amfana da wannan karamcin kuwa, sun hada da Afghanistan da Benin da Burkina Faso da jamhuriyar Afrika ta tsakiya da Chadi da Comoros da jamhuriyar demokradiyyar Congo, sai Gambia da Guinea.

Sauran sun hada da Guinea-Bissau da Haiti da Laberiya da Madagaska da Malawi da Mali, sai Nepal da Niger da Rwanda da Sao tome da Pricippe da Saliyo da Solomon Island da Tajikistan da Togo da kuma Yemen.

Saidai kuma babu Nijeriya cikin jerin kasashen da wannan tallafi ya shafa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply