Home Sabon Labari Babu rashin tsaro a hanyar Kaduna zuwa Abuja-Yan sanda

Babu rashin tsaro a hanyar Kaduna zuwa Abuja-Yan sanda

108
0

Taskar Guibi: Karanta Takaitattun Labaru 27.12.2019

 

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin juma’atu babbar rana, talatin ga watan Rabiul/Rabiyul Sani, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da ashirin da bakwai ga watan Disamba, na 2019.

1. Yau ma’aikata ke komawa bakin aiki bayan hutun da aka sha na kirsimeti. Da ma gwamnatin tarayya ta sanar da shekaranjiya laraba da jiya alhamis a matsayin ranakun hutu.

2. Hukumar ‘yan sanda ta jihar Kaduna ta bai wa talakawa matafiya da ke bin hanyar Kaduna zuwa Abuja tabbacin ta dauki matakan kare rayukansu daga hannun kidinafas da makasa da ke ci gaba da cin karensu babu babbaka a hanyar, har ake zargin kidinafas din ne suka firgita manyan janarorin soja matafiya suka koma suna bin jirgin kasa na Kaduna zuwa Abuja, da kuma Abuja zuwa Kaduna.
An ta zargin cewa janarorin sojan da suka kauracewa hanyar saboda tsoron kidinafas, da za su cire tsoron su dinga bin hanyar, da tuni an dade da daina kidinafin ko kashe talaka a hanyar.

3. Janar Buratai ya ci gaba da kira ga sojoji su ci gaba da jajircewa don bai wa ‘yan kungiyar Boko Haram kashi kamar yadda suka nuna bajinta a ‘yan kwanakin nan a jihar Yobe da jihar Barno.

4. Ma’aikatan gwamnatin tarayya na ci gaba da dakon ariyas na sabon albashi da gwamnatin tarayya ta musu alkawarin za ta biya kafin karshen wannan watan. Yau dai ashirin da bakwai, wato saura kwana hudu watan ya kare. Wasu ma’aikatan sun ga dilin-dilin na watan Disamba tsoho wasu kuma sun ga sabo.

Da fatan za a yi hakuri yau ma labarun ba yawa saboda a lokaci irin wannan na shagulgula, labarun kan yi karanci.

Af! Da nake shawagi a fesbuk na ga zawarawa da ‘yan mata na ta korafin adimishan na bana na shiga ABU ya gama fitowa ba sunansu. Wato adimishan na Aure Bautar Ubangiji, ga shekarar ta kare ba su samu mijin aure ba. Sai kuma shekarar 2020 su ci gaba da nema ko za su samu shiga.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

 

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply