Home Siyasa Shariar Zakzaky: Babu ruwana da maganar shariar Zakzaky inji Buhari

Shariar Zakzaky: Babu ruwana da maganar shariar Zakzaky inji Buhari

101
0

 

Shugaban yayi magana ne ta bakin Garba Shehu babban mai magana da yawunsa. A cikin sanarwar da ofishin Garba Shehun ya fitar da yammacin Jumaar nan, gwamnati tace bata da hannu a cikin shariar da ake yiwa jagoran yan shia Ibrahim Zakzaky.

Shugaban yace ci gaba da zanga zanga da yunkurin tayar da hankulan jamaa da yan shia ke yi ba za su sanya shi yiwa kotu katsalandan ba ko kuma ya sa a kaucewa kaida.

Sannan kuma shugaba Buhari ya bukaci yan shia da su daina zanga zanga a Abuja bayan shariar da ake yiwa jagoran nasu tana jihar Kaduna. Ya kuma ce ba ma daidai bane magana tana kotu sannan kuma su fito fili suna zage zage da yunkurin tunzura tashin hankali.

Sanarwar ta shawarci yan shia tun da magana tana kotu su ci gaba da bayar da karfi ga kotu wurin samar da hujjoijin da za su cimma burinsu.

Yaya kuke kallon wannan shawara?

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply