Home Labarai Babu sassauci tsakaninmu da ‘yan ta’adda-El Rufa’i

Babu sassauci tsakaninmu da ‘yan ta’adda-El Rufa’i

161
0

Gwamna jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-rufai ya sha alwashin sanya kafar wando daya da ‘yan bindigar da ke kai hare-hare a jihar.

Kazalika gwamnan ya shaida wa manoman jihar cewa dole ne gwamnatinsa ta kawo karshen ayyukan ta’addanci a jihar kafin daminar bana ta kankama.

Da ya ke kaddamar da rabon takin zamani ga manoman jihar, Malam Nasir ya ce zama wajibi jihar ta dakile ayyukan ‘yan bindiga domin samar da zaman lafiya a jiha.

Yace ba a za a saurara wa masu aikata ba ko kadan ba, kuma babu maganar sulhu, illa-iyaka a murkushe su.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply