Home Labarai Babu takamaiman ranar bude sansanonin matasan NYSC

Babu takamaiman ranar bude sansanonin matasan NYSC

88
0

Hukumar kula da matasa masu yi wa kasa hidima ta Nijeriya NYSC ta ce har yanzu babu takamaiman ranar bude sansanonin matasan masu hidimtawa kasa.

A cikin wata takarda da ya aike wa Daily Trust, mai magana da yawun hukumar Adenike Adeyemi, ya musanta wasu labarai da ake yadawa cewa za a bude sansanonin a ranar 27 ga watan Oktoba, 2020 don daukar matasa ‘yan rukuni na “A”.

Ta ce babu kanshin gaskiya a labaran, inda ta bukaci matasan da sauran al’umma da su yi watsi da su.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply