Home Labarai Babu wanda ya mutu a harbe-harben da aka yi a Lekki –...

Babu wanda ya mutu a harbe-harben da aka yi a Lekki – Sanwo-Olu

97
0

Gwamnan jihar Lagos Babajide Sanwo-Olu ya ce babu wanda ya rasa ransa a harin da aka kai daren Talata a Lekki da ke birnin Lagos.

Gwamnan ya sanar da hakan a wani jawabin kai tsaye da ya gudanar a ranar Laraba, inda ya ce mutane biyu ne kacal aka ji wa rauni, kuma su ma an yi musu magani.

Ya ce sai sauran wadanda suka guggurje yanzu haka su na amsar magani a asibitoci daban-daban na jihar.

Sanwo-Olu ya ce sojoji ne suka bude wa masu zanga-zangar EndSARS wuta, abin da ya tunzura matasan, ya ce yanzu haka yana tattaunawa da shugabannin sojojin domin shawo kan lamarin.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply