Home Lafiya Bahaya a Kasa: Asusun UNICEF ya ce Nijeriya ce ta biyu a...

Bahaya a Kasa: Asusun UNICEF ya ce Nijeriya ce ta biyu a duniya

74
0

Daga Abdullahi Garba Jani

 

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya -UNICEF- ya ce Nijeriya ce ta biyu wajen yin bahaya a kasa da yawan mutane milyan 47 masu wannan dabi’a.

Jami’in watsa labaran -UNICEF- a Nijeriya Dr Geoffrey Njoku, ya fada wa kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya cewa a shekarar bara ta 2018 wani bincike ya tabbatar da cewa kusan kaso 24% na yawan mutanen Nijeriya na bahaya a kasa.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya ya ba da rahoton cewa a shekarar 2018 kasar ta kaddamar da gangamin yaki da bahaya a kasa. Amma masu sharhi na cewa har yanzu babu abin da ya sauya.

Rashin wuraren yin bahaya na jama’a a kasuwanni da sauran wuraren haduwar jama’a na ci gaba da sanya mutane yin bahaya a duk inda suka sami sukuni. Abin da ke barazana ga muhalli da lafiyar dan adam. Bayan haka wannan dabi’ a ta bahaya a kasa ta kan taba mutumcin jama’a a duk lokacin da mai bahayan ya hadu da wanda ya san sa.

Hoton gargadin kada ayi fitsari

A sakamakon yadda wasu ke bahaya da fitsari a duk inda suke so, a wasu gidaje ko ofisoshin gwamnati akan rubuta cewa ba a fitsari ko bahaya anan.

Kasar Indiya ce ta farko a bahaya kasa, inda Nijeriya ke bi ma ta a matsayin ta biyu, lamarin da ake ganin yana bukatar daukar matakin gaggawa don magance shi.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply