Shugaban ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS) a Nijeriya, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya yi kira ga Musulmi da Kiristocin Nijeriya da su mutunta addinan juna, tare da haɗa kai wajen kare ƙasar.
Sheikh Bala Lau ya ce Musulmi da Kiristoci duk suna da haƙƙi da ruwa da tsaki a Nijeriya, don haka ya kamata su zauna lafiya duk da bambance-bambancen addininsu.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ya bayyana hakan ne ranar Juma’a a filin jirgin sama na Abuja, bayan tafiyar Sakataren-Janar na kungiyar kasashen Musulmi ta Duniya, Sheikh Dr Mohammed bin Abdulkarim Al-Issa.
An gudanar da taron ƙasa da ƙasa na tsawon kwanaki biyu kan bambancin ra’ayi da zaman lafiya a tsakanin al’umma, wanda JIBWIS ta shirya tare da haɗin gwiwar ķungiyar kasashen Musulmi ta Duniya.
Sheikh Bala Lau ya ce manufar taron ita ce ƙarfafa zaman lafiya, fahimtar juna da kwanciyar hankali a Nijeriya, Afirka ta Yamma da sauran sassan nahiyar Afirka.
Ya ce duk da bambancin addini da al’adu, ’yan Nijeriya suna da manufa guda ta tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai.
“Duk da bambancinmu, muna da manufa guda, manufarmu ita ce mu zauna cikin zaman lafiya da jituwa, kai ka yi addininka, ni kuma in yi nawa, babu tilastawa a cikin addini,” in ji shi.
Sheikh Bala Lau ya jaddada cewa babu wani ɓangare da ke da ikon korar ɗayan daga Nijeriya, domin ƙasar ta kowa ce.
Ya ce ya kamata Musulmi su mutunta addinin Kiristoci, su kuma mutunta nasu addinin, domin haɗin kan jama’a shi ne ginshiƙin kare ƙasar.
Shugaban JIBWIS ɗin ya kuma yi kira ga ’yan Nijeriya da su koyi darasi4 daga yadda Annabi Muhammad (SAW) ya zauna lafiya da mabiya sauran addinai a Madina.
Ya bayyana cewa sanarwar da aka fitar bayan taron ba za ta tsaya a kan takarda ba, inda ya ce za a kafa wani kwamiti da zai sa ido kan yadda za a aiwatar da abubuwan da aka amince da su.
A nasa jawabin, Sheikh Al-Issa ya yi gargaɗi kan tsattsauran ra’ayi, tare da kira ga ’yan Nijeriya da su kare mutuncin ɗan Adam tare da ƙin duk wani yunƙuri na amfani dar addini, ƙabila ko talauci wajen raba al’umma.
