Home Wasanni Bakary Papa Gassama ne zai hura wasan Nigeria da Algeria a cin...

Bakary Papa Gassama ne zai hura wasan Nigeria da Algeria a cin kofin nahiyar Africa

111
0

Afcon 2019: BAKARY PAPA GASSAMA NE ZAI HURA WASAN NIJERIYA DA ALJERIYA A GASAR CIN KOFIN NAHIYAR AFRIKA.

Shahararren mai hura wasan na nahiyar Afrika Bakary Papa Gassama ne zai hura wasan da za a taka a daren yau Lahadi tsakanin Nijeriya da Kasar Aljeriya.

Nijeriya da Aljeriya dai za su hadu ne a wasan dab da na karshe (semi final) wanda jamaa da dama ke kallon zai yi zafi sosai domin duk wanda yayi nasara shi ne zai shiga zagayen karshe wanda za’a fara a ranar juma’a.

Bakary Gassama dai dan asalin kasar
Gambia ne wadda ba ta samu damar zuwa gasar ba a wannan shekara.

Ba ya ga Najeriya da Aljeriya, kasar Senegal ma za ta kece raini da kasar Tunisia a maraicen yau a neman gurbin zuwa wasan karshe na gasar.

Wace kasa kuke ganin za ta iya kaiwa zagayen karshe na gasar?

#AgJ

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply