Home Labarai Ban ce zan tsaya takarar shugaban ƙasa ba – Tinubu

Ban ce zan tsaya takarar shugaban ƙasa ba – Tinubu

201
1

Jagoran jam’iyyar APC na ƙasa Bola Tinubu, ya yi kira ga rusassun wakilan kwamitin aiki na jam’iyyar APC da su amince da hukuncin shugaba Buhari.

Ya kuma buƙace su da su sake nuna jajircewar su don tabbatar da manufofin da aka kafa jam’iyyar.

Tinubu wanda ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a ranar Asabar, ya ce har yanzu bai yanke shawarar tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023 ba.

Akwai dai hasashe mai ƙarfi da ake da shi na cewa tsohon gwamnan na Lagos na da muradin zama magajin shugaba Buhari a babban zaɓen 2023.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

1 COMMENT

  1. A gaskiya mutane da dama ciki kuwa har da ni muna hasashen cewa Tinubu nada muradin tsayawa takara a tutar jam’iyyar Apc ganin yanda yake da karfin fada aji a jam’iyyar.
    To sai dai masana da masu sharhi na ganin cewa ba lallai bane hakarsa ta cimma Ruwa sakamakon cire Adams oshumole gada shugabancin jam’iyyar.
    Umar farouk ibrahim daga katsina

Leave a Reply