Mataimakin shugaban kasa Prof Yemi Osinbajo ya ce babu kamshin gaskiya a cikin labarin da ke cewa ya amshi kudi da suka kai darajar Naira milyan dubu 4 (N4bn) daga Ibrahim Magu.
A cikin wata takarda daga mai magana da yawun mataimakim shugaban kasar Mr Laolu Akande ta ce wannan labari ba ya da tushe bare makama.
Wani rahoto ya yi zargin cewa Mr Ibrahim Magu tsohon shugaban hukumar hana yi wa tattalin arzikin kasa tu’annati EFCC ya fada wa kwamitin da ke bincikensa cewa ya ba mataimakin shugaban kasa kudi Naira milyan dubu 4.
