Sakataren jam’iyyar ADC a Nijeriya Rauf Aregbesola, ya ce tun bayan aurensa da matarsa, Sherifat, bai taba neman yin mu’amala da wata mace daban ba.
Tsohon gwamnan jihar Osun ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a wani gangamin yaƙin neman zaɓe na ADC a ƙaramar hukumar Ejigbo ta Jihar Osun, gabanin zaɓen gwamnan jihar da za a gudanar ranar 15 ga Agusta, 2026.
Aregbesola, wanda ya yi jawabin cikin harshen Yarbanci, ya ce amincinsa ga matarsa na daga cikin alkawarin da ya ɗauka tsakaninsa da Allah.
Ya ce tsoron Allah da kuma addininsa ne suka sa ya kasance mai aminci ga matarsa tun bayan aurensu.
A cewarsa, ba kowane namiji ne zai iya yin irin wannan ikirari ba, amma ya ce yana alfahari da kasancewa mai aminci ga matarsa.
Aregbesola ya ce: “Ya Ubangijina Allah, idan kai ne wanda nake bautawa, kuma ban ƙara wani abu a kan hakan ba, abin da zan faɗa yanzu, ƙalilan daga cikin maza ne za su iya faɗa, saboda tsoronka, ban taba yin lalata da wata mace ba tun bayan da na auri matata.”
Ya kuma bayyana cewa ya yi wa Allah alkawarin cewa a watan Yuni na shekara mai zuwa, za su gudanar da wani abu a fadar Gwamnatin jihar Osun.
Wannan furuci na Aregbesola na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyun siyasa ke ƙara zafafa yaƙin neman zaɓe a jihar Osun, gabanin zaɓen gwamnan jihar.
Zaɓen na ranar 15 ga Agusta wanda ɗan takarar Gwamna Ademola Adeleke na Accord Party, ke neman wa’adi na biyu, da ɗan takarar APC, Bola Oyebamiji, da kuma ɗan takarar ADC, Najeem Folasayo Salaam.
Zaɓen zai gudana ne a faɗin ƙananan hukumomi 30 na Jihar Osun.
