Home Kasashen Ketare Banbancin yare ya hana yanke hukunci a kotun Kamaru

Banbancin yare ya hana yanke hukunci a kotun Kamaru

210
0

Banbancin yare ya kawo tsaiko a lokacin sauron shari’ar da jagoran harshen turanci a Kamaru Sisiku Ayuk Tabe da wasu 9 suka daukaka kan hukuncin kisa da aka yanke masu.

An dai kama su ne da laifi a zarge-zarge 10 da ake yi masu da suka hada da ta’addanci da bata dukiyar jama’a, a rawar da suka taka ta ‘yan tawayen ‘yan aware a sassan kasar biyu da ke magana da harshen turanci a akasar da mafi yawan jama’arta ke Magana da yaren Faransa.

A  farkon sauraron shari’ar dai, da yawa daga cikin ‘yan awaren sun rika nuna yatsunsu zuwa ga kunnuwansu, alamun ba su jin abunda alkalin wanda ke magana da faransanci ke cewa.

Kwatsam alkalin ya kawo karshen zaman, bayan ya yi watsi da bukatar wadanda ake zargin na neman a yi Magana da harshen turanci sannan ya dage karar zuwa watan Agusta.

Lauyoyin da ke kare wadanda ake zargin dai sun soki alkalin da wannan hukunci da yanke, wanda suka ce ya saba da kundin tsarin mulkin kasar wanda ya bada damar alkalai su rika gudanar da shari’a a yaren da wanda ake zargi ke fahimta matukar bai saba da yardaddun yarukan kasar na Turanci da Faransanci ba.

 

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply