Home Labarai Bandit sun kashe mutum 9 a Kaduna

Bandit sun kashe mutum 9 a Kaduna

135
0

Akalla mutum 9 ne aka kashe a wani harin da ake zargin ‘yan bindiga dadi da kaiwa a kauyen Avong Doka da ke karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.

Wannan dai na zuwa ne mako guda, bayan da ‘yan bindigar suka kona gidaje da dama a wata ruga da ke kauyen Agwala Dutse duk dai a cikin karamar hukumar ta Kajuru.

Duk da cewa dai Rundunar ‘yan sandan Kaduna bata tabbatar da harin ba, shugaban karamar hukumar Kajuru Cafra Caino ya shaidawa Channels Television cewa ‘yan bindigar sun dirarwa kauyen ne da Asubahin yau Laraba, kuma suka fara harbin kan mai uwa da wabi, wanda ya tilasta jama’ar kauyen guduwa don tsira da rayuwar su.

Ya ce mutum 9 ne suka mutu sakamakon harbin bindiga yayin da, da dama suka jikkata, kuma suna asibiti don a yi masu magani.

Ya ce ba don sojoji sun zo da wuri ba, wanda hakan ya sanya ‘yan bindigar suka gudu cikin daji, da adadin wadanda za su mutun sai ya zarta hakan.

Ya kara da cewa an kuma jibge sojojin a kauyen da hana sake faruwar wani harin.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply