Home Labarai Bani da hannu ko masaniya a karin harajin 7.5% VAT kan wayoyin...

Bani da hannu ko masaniya a karin harajin 7.5% VAT kan wayoyin sadarwa – Pantami

68
0

Ministan sadarwa Dr Isa Ali Pantami ya ce bai da masaniya a karin kudin harajin kashi 7.5% na VAT da aka yiwa wayoyin sadarwa a Nijeriya.

Dr Isah Ibrahim Pantami, Ministan sadarwar Nijeriya

Ministan ya umarci kamfanonin sadarwar kasar da duk masu korafi, su kai koken su ga hukumar tattara kudaden haraji ta FIRS kan duk wani karin bayani da suke nema na karin kudin harajin.

Pantami, ya ce hukumar ita ked a alhaki kan duk wasu bayanai da suka shafi haraji.

A cikin wata sanarwa da mai Magana da yawun ministan Uwa Suleiman ta fitar a jiya, Pantami, ya ce ba shi aka dorawa alhakin bibiyar harajin na VAT ba.

Sanarwar ta ce “bayan nuna godiya ga ‘yan Nijeria da suka nemi karin bayani kan wannan sabon tsari, mai girma ministan sadarwa na sanar da jama’a cewa maganar karin harajin VAT ba a karkashin ma’aikatar mu yake ba”.

Pantami ya ce bai da wata masaniya, ko tuntubar ofishin sa kafin daukar wannan mataki na kara kudin haraji ga masu amfani da wayoyin sadarwar.

A don haka, ya ce duk mai wani koke, ko neman karin bayani, ya tuntubi hukumar tattara kudaden harajin.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply