Home Labarai Bankin duniya ya ware $346 don gudanar da ayyuka a Nijeriya da...

Bankin duniya ya ware $346 don gudanar da ayyuka a Nijeriya da wasu ƙasashe

222
0

Bankin duniya ya amince da bada $346m domin gudanar da wasu manyan ayyuka biyu na kyautata rayuwar jama’a, a ƙasashen yankin tafkin Chadi.

Wata sanarwa daga bankin ta yi bayanin cewa ayyukan waɗanda za a samar da kuɗaɗen su ta hanyar ƙungiyoyin ci gaba, za a raba su ne tsakanin ƙasashen Nijeriya, Nijar, Kamaru da Chadi.

Ayyukan farfaɗo da yankunan da rikici ya tarwatsa a yankin Arewa maso gabashin Nijeriya, wanda za a kashe $176m zai taimakawa gwamnatin Nijeriya wajen inganta harkokin rayuwa a jihohin Adamawa, Borno da Yobe.

Aikin kuma zai tamaika wajen daidaituwar al’amura a yankin ƙasashen tafkin na Chadi.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply