Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi Bankin duniya zai ba Nijeriya bashin $1.5bn

Bankin duniya zai ba Nijeriya bashin $1.5bn

123
0

Bankin duniya ya amince da ba Nijeriya bashin Dala biliyan $1.5bn

Bankin ya ya faɗi haka ne a wata sanarwa da ya fitar a Talata yana mai cewa bashin na da nufin tallafawa ƙoƙarin Nijeriya na rage talauci.

Hukumar gudanarwar daraktocin babban bankin ne dai ta amince da bada bashin kan ayyuka biyu, da suka haɗa da matakin da gwamnatin Nijeriya ke ɗauka na farfaɗo da tattalin arziƙi wanda Covid-19 ta ɗaiɗaita da kuma shirye-shiryen ayyukan ci gaba daga matakin jihohi.

Bankin ya ƙara da cewa Nijeriya na cikin mawuyacin hali saboda haka ba ƙasar bashin zai taimaka sosai

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply