Manajan Daraktan Bankin Ja’iz Hassan Usman, ya bayyana cewa bankin ya samu izinin kafa karin sabbin rassa uku a duk fadin kasar.
Malam Hassan Usman, ya bayyana hakan ne yayin da ya ke zantawa da manema labarai a Abuja.
Ya ce wadannan sabbin rassan na a matsayin kari ga kafitanin rassa 41 da da bankin ke da su a duk fadin kasar nan.
To sai dai kawo yanzu Usman din bai bayyana wuraren da za su gina wadannan sabbi rassa guda 3 ba.
