‘Yan bindiga da dama ne aka tarwatsa kuma aka lalata makaman su a wani harin sama da rundunar Hadarin Daji ta kai a jihar Zamfara.
Jami’in yada labaran rundunar Major General John Enenche ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.
Ya ce an kai harin ne a maboyar ‘yan bindigar guda biyu da ke Tsibiri da Manya duk a karamar hukumar Zurmi, a ranar Asabar, a karkashin shirin hare-haren ba sani ba sabo na kawar da ‘ya bindiga a yankunan Arewa maso yamma, da kuma Arewa ta tsakiya.
