Home Labarai Barayi sun sace sandar majalisar Ogun

Barayi sun sace sandar majalisar Ogun

132
0

Wasu da ake zargin barayi ne sun sace sandar majalisar dokoki ta Ogun a safiyar ranar Alhamis.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a Abeokuta, jami’in hulda da jama’a na rundunar ƴansandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi ya bayyana cewa barayin sun kutsa kai cikin ofishin kakakin majalisar ta rufin saman inda suka yi awon gaba da sandar.

Kakakin majalisar, Olakunle Oluomo, wanda shi ma ya tabbatar da labarin, ya bayyana cewa har yanzu ba a san dalilin barayin na sace wannan sanda ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply