Home Sabon Labari Barcelona na fuskantar durƙushewar tattalin arziƙi

Barcelona na fuskantar durƙushewar tattalin arziƙi

33
0

Barcelona ta nemi lamunin bankunan da ke bin ƙungiyar bashi, su jinkirta mata saboda kaucewa rushewar tattalin arziƙin ƙungiyar.

Yanzu haka dai ƙungiyar tana da alhakin biyan bashin fam miliyan £400m a cikin watanni 12 masu zuwa, yayin da gaba ɗaya ƙarfin jarinta bai wuce £600m ba.

Wannan dai na nuni da dole sai ƙungiyar ta samar da ƙarin hanyoyin samun kudi8da suka haɗa da sayar da Messi, sayar da ƴancin sunan filin wasan Camp Nou ko kuma shigo da ƙarin masu zuba jari da ke son haɗa guiwa da ƙungiyar.

Saidai wannan zai faru ne kaɗai bayan an yi zaɓen shugaban ƙungiyar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply