Home Sabon Labari Barcelona Ta Bada Aron Coutinho a Jamus

Barcelona Ta Bada Aron Coutinho a Jamus

58
0

Daga: Ahmadu Rabe ‘Yanduna/NIB

Bayern Munich ta ɗauki Philippe Coutinho daga Barcelona a matsayin aro na shekara ɗaya, tare da zaɓin sayen sa idan har ƙungiyar na da buƙata, a ƙarshen yarjejeniyar.

Barcelona ta ce ƙungiyar Bayern Munich dake Jamus za su biya fam miliyan 7.78 domin ɗaukar ɗan wasan na Brazil, mai shekara 27, sannan za su iya sayen sa a kan fam miliyan 109.84.

Bayern za kuma su biya albashin Coutinho na tsawon lokacin da zai shafe a Jamus.

Coutinho ya koma Barcelona ne daga Liverpool kan fam miliyan 142 a watan Janairun 2018.

Duk da cewa ya zura kwallo 21 a wasa 76 a Sifaniya, ɗan wasan ya gaza cimma burin da aka ɗora masa tun farko, abin da ya sa aka riƙa alaƙanta shi da komawa wasu ƙungiyoyi ciki har da Liverpool da Arsenal da kuma Tottenham.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply