Home Sabon Labari Barcelona za ta hana Messi zuwa ko ina – Nadal

Barcelona za ta hana Messi zuwa ko ina – Nadal

81
0

Toni Nadal, Kawu kuma tsohon kocin dan wasan tennis mai rike da kambun Lashe gasar Tennis 20 Rafa, ya yi kira ga kungiyar Barcelona ta yi kokarin shawo kan Lionel Messi ya ci gaba da zama a kungiyar.

Nadal ya hada karfi da dan takarar shugaban kungiyar a Barcelona Victor Font gabanin zaben da ke tafe.

Idan Font ya ci zaben shugaban kungiyar, Nadal zai kasance mai kula da hulda da hukumomi kuma zai jagoranci wani sabon sashen da aka kirkira don inganta kyawawan halaye tsakanin ‘yan wasan matasa.

Kuma ya ce daya daga cikin abubuwan da zai ba fifiko shi ne tabbatar da shahararren dan wasan kungiyar Lionel Messi ya ci gaba da zama a Barca, duk da dai ba shi da tabbas ko zai iya yin hakan.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply